(ABNA24.com) Dubun dubatan masoya Ahlul baiti ne suka yi tururuwa a hubbaren Imam Ridha (AS),limami na 8 daga cikin jerin limaman shiriya 12 na iyalan gidan Manzon Allah, Tsira da aminci su tabbata gare shi da iyalensa, dake birnin Mashhad mai tsarki na kasar Iran, domin juyayin zagayowar ranar shahadarsa.
Har ila yau an gudanar da irin wadannan tarurrukan na juyayin zagayowar shahadar Imam Ridha, a wasu kasashe daban - daban na duniya.
Iman Redha, ya yi shahada ne a hannun sarki Ma’amum daya daga cikin sarakunan abbasiyawa sakamakon shayar da shi guba.
Da yake bayani game da zagayowar shahadar ta Imam Ridha, jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamna’i ya ce, kuma akwai darrusa masu yawa da zamu koya a rayuwar Iman Redha, don haka babban sakon da rayuwarsa take isarwa gare mu shi netsayin daka da gwagwarmaya ba tare da gajiyawa ba.
/129
30 Oktoba 2019 - 06:24
Lambar labari: 985055
Dubun dubatan masoya Ahlul baiti ne suka yi tururuwa a hubbaren Imam Ridha (AS),limami na 8 daga cikin jerin limaman shiriya 12 na iyalan gidan Manzon Allah, Tsira da aminci su tabbata gare shi da iyalensa, dake birnin Mashhad mai tsarki na kasar Iran, domin juyayin zagayowar ranar shahadarsa.